JAMI'AN HUKUMAR DMCSA SUN KAI ZIYARAR AIKI RUMBUNAN ADANA MAGUNGUNA NA SHIYYOYI
Daga Farouk Isa Musa
Darakta-Janar na hukumar ta DMCSA Famasist Gali Sule, ta bakin Jami'in Hulda da Jama'a na ma'aikatar Farouk Isa Musa, ya ce sun kai ziyarar ne don ganewa idanunuwansu yanda ayyuka suke gudana a shiyyoyin guda 4.
Famasist Gali Sule ya kara da cewa ziyarar tana da matukar muhimmanci, domin a lokacin ziyarar ne ake fahimtar nasarori da aka samu, da kuma irin kalubale da rumbunan adana magunguna na shiyyoyi ke fuskanta.
Bugu da kari, Famasist Gali Sule ya ce jami'an ma'aikatar suna kai irin wannan ziyarar gani-da-ido daga lokaci zuwa lokaci don tabbatar da komai yana tafiya kamar yanda ya kamata.
Daga nan sai ya jaddada kudirin gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf na samar da wadatattu kuma ingantattun magunguna masu rahusa a dukkanin asibitocin da ke jihar nan.
A karshe, Darakta-Janar na Hukumar Samar da Magunguna ta Jihar nan ya yi kira ga ma'aikatan hukumar da su kasance masu gaskiya da rikon amana a yayin gabatar da ayyukansu domin samun al'umma mai cike da koshin lafiya, wanda hakan zai samar da cigba mai dorewa.
Comments
Post a Comment