KUNGIYAR PHARMACIST GALI SULE/ABBA GIDA-GIDA SUPPORT GROUP TA SHA ALWASHIN YIN AIKI TUKURU DON SAMUN NASARAR APC A ZABEN 2027
Daga Wakilinmu Kungiyar Pharmacist Gali Sule/Abba Gida-Gida Support Group ta sha alwashin yin aiki ba dare ba rana domin ganin jam’iyyar APC ta samu gagarumar nasara a zabukan kasa na shekarar 2027. Darakta Janar na Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Aikin Asibiti ta Jihar Kano (DMCSA), Pharm. Gali Sule, ya bayyana haka ne a lokacin da ya jagoranci shugabannin kungiyar don kai wa Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Karamar Hukumar Nassarawa, Hon. Hassan Hussain, ziyara a ofishinsa. Da yake jawabi, Pharm. Gali Sule, wanda shi ne uba kuma jagoran kungiyar, ya bayyana cewa sun kai ziyarar ne domin karfafa alaka da kuma tattauna hanyoyin da za a bi wajen yin aiki tare, domin tabbatar da hadin kai da nasarar jam’iyyar APC da daukacin ‘yan takararta a zaben 2027. Ya ce wannan ya hada da kokarin ganin jam’iyyar ta samu nasara tun daga matakin Shugaban Kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Alhaji Kashim Shetima, zuwa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf da mataimak...