Aisha Saji Ta Kai Ziyarar Gani da Ido Zuwa Hukukomin Guda Biyu
Daga Amina Lawan Isah Kwamishiniyar Yawon Bude da Al'adu Aisha Lawan Saji Rano wanda ta gudanar da ziyarar ne a yau Talatin ga watan Disamba na shekarar 2024 ta Kai wa Hukumar Adana Tarihi da Al'adu da Kuma Hukumar Yawon Bude Ido,Ziyarar ta bayu ne Domin duba yanayin yadda suke Gudanar da ayyukansu da Kuma ganin yadda za'a ciyar da Hukumomin gaba A Lokacin da ake Gudanar da Ziyarar kwamishiniyar Hajiya Aisha Lawan Saji ta Yaba da Kokarin da Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf yake a wannan Hukumomin dake Karkashin Ma'aikatar Yawon Bude Ido da Al'adu Don ganin An Bunkasa Al'adu Ta Kara da cewa ta ga duka Hukumomin An gyara ginunsu sun dawo sababbi Saji ta Yaba da irin Kokarin da suke na ganin sun ciyar da Hukumomin Gaba da kirkiro sababbin Abubuwan Al'ada da dawo da na da, da aka manta Domin ciyar da ma aikatar Gaba Kwamishiniyar ta Yi Kira Ga daukacin Ma'aikatan Hukumomin Yawon Bude Ido da Raya Al'adu da s...